A Yammacin wannan rana ta lahadi 16/2/2025
Mai girma Kwamishinan Kasuwanci na jihar Kano Hon. Gwani Shehu Sagagi Ya karbi kunshin shugabanci na riko na Sharada Small Scale Industry wanda suka kawo masa ziyarar girmamawa a matsayin na Uba kuma Jagora,
A Jawabinsa Shugaban riko na Sharada Small Scale yayi godiya ga Allah da mai girma Gwamana Alh Abba K Yusuf bisa saka kwarya a gurbinta, wanda haka yasa yanzu har an samu sauyi ta fannin kasuwanci a jihar Kano
Kwamishinan yaja hankalin su da su zamo shuwagabannin adalai da kuma jajir cewa wajan kawo abin arziki ga masu ƙaramin karfi a Sharada Small Scale, ya kumayi godiya ta musamman da wannan ziyarar da suka kawo masa, ya kuma sanar musu cewa tuni shirye-shirye sukayi nisa na samar da mugudanar ruwa a cikin Kasuwannin jihar Kano.
Muna addu’ar Allah Ubangiji ya kara tabbatar maka da dukan nasara da alheri Ameen Bijahi Sayyidil mursalina saw
Muhsin Kmc
Personal Assistant
on Media
16/2/20250
By:
Posted in: