
Alhaji Umar Musa Sake Kwankwaso
Sarautar MAJI DADI sarauta ce Ta kasar zazzau Wato An farata ne A masarautar zazzau Asalin MAJI DADI a zazzau Sarautar yaron sarki Ce Wanda sarki ke so Kuma yake kauna Kuma ya Amince da shi domin MAJI DADI na iya shiga ko Ina a gidan sarki saboda Aminci da kauna dake tsakanin sa da sarki MAJI DADI nada Alfarma sosai a wajen sarki Kuma An fara wannnn sarauta a zazzau tin zamanin sarakunan habe Abinda yasa aka Kira shi da MAJI DADI shi shi shine Mai jiyar da sarki Dadi ta fuskar Ayyukansa Domin shine Mai kula da Abubuwan na yau da gobe na sarki tindaga kan Abinci da kayan sawa da hidimar bakin sarki da sauran su a taikace MAJI DADI shine Kamar jami’in walwala da jindadi na sarki wannan Aiki da yake shine yasa ake kiransa Maji Dadi a wata ruwayar Kuma Ance kalmar MAJI DADIN kirari ne ake yiwa Mai yin wannan Aiki da muka Ambata A sama daganan Kuma yazama sarauta Sarautar MAJI DADI tanan anayinta a zazzau har yanzu Kuma tayadu Ana yinta A sauran masarautu Sarautar MAJI DADI anayinta a kusan duka masarautun kasar Hausa Kuma Ana yinta da fuskoki Kamar guda uku Anayinta matsayin cikkaken Hakimi da Hakimin Hakimi da Kuma yaron gidan Hakimi Wato bara MAJI DADI sarauta ce ta Alfarma Anayiwa Yan kasuwa da yantakarda da masu Damara a mafi yawan Lokaci
Kamar saraun sarautu itama Sarautar MAJI DADI masartan fada suna Yi Mata kirari da cewa JIYAU MAI FADA JIYAU MAI SARKI JIYAU DAMAMA YOLA MAMA JINDADI DAGA ALLAH JIN DADIN ALLAH SAI KARI
✍️DAGA ZAUREN DAGA MASARAUTUNMU
07039217236